24 Faburairu 2022 - 14:41
​Rwanda: Shugaba Kagame Yana Ziyarar Kwanaki Biyu A Mauritaniya

Shugaban kasar Rwanda Mr Paul Kagame ya fara ziyarar aiki na kwanaki biyu a kasar Mauritaniya a jiya Laraba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar ‘The New Times’ ta kasar Rwanda ta bayyana cewa bayan isarsa babban tashar jiragen sama na Nouakchott, shugaban kasar Mauritaniya Mohammad Wald Ghazouani ne ya tarbe shi. Sannan shuwagabannin biyu suka kebe su biyu na wani lokaci kafin tawagogin kasashen biyu su tattauna a tsakaninsu.

Labarin ya kara da cewa ana saran shuwagabannin kasashen biyu da jami’an gwamnatocinsu zasu rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama a cikin ziyarar kwanakin biyun da Kagame ya ke yi a birnin Nouakchott.

Majiyar fadar shugaban kasa a birnin Kigali ta fadawa jaridar ‘The New Times’ na Rwanda kan cewa ana saran kasashen biyu zasu rattaba hannu kan takardun fahintar juna a bangarorin tsaro, sadarwa, Ma’adiai, Noma da kuma Zuba jari.

342/